Masu Ruwa da Tsaki na Jam’iyyar PRP a shiyyar Arewa maso Yamma ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ƙoƙarin mallake tikitin takarar jam’iyyun siyasa daban-daban ta hanyar sayen fom ɗin takara ga masu neman mukamai.
Shugaban masu ruwa da tsakin, Abdullahi Musa Giza, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano.
A cewarsa, mutum guda wanda ba mamba ba ne a jam’iyyar PRP ya saye fom ɗin takara na dukkan mukamai 69 na jam’iyyar, lamarin da ya ce ya tayar da hankalin masu ruwa da tsaki.
Giza ya ce akwai rahotannin da ke alakanta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wannan tsari, yana mai gargadin cewa irin wannan mataki na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya da kuma tsarin gudanar da harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ko wakilansa kan zarge-zargen da aka yi masa.