PRP ta bukaci Tinubu ya yi murabus kan tabarbarewar tsaro a Najeriya

Jam’iyyar PRP ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus daga mukaminsa, tana mai zargin gwamnatinsa da gaza magance matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar sassan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya fitar, PRP ta ce tabarbarewar tsaro a fadin kasar nan ta nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Jam’iyyar ta bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka sun ci gaba da karuwa, lamarin da ya sa al’umma daga kowane bangare na kasar ke rayuwa cikin fargaba.

A cewar PRP, babu wani dan Najeriya da ya tsira daga barazanar rashin tsaro, inda ta ce manyan jami’an gwamnati, sojoji da fararen hula, har ma da yara kanana, na fuskantar hare-hare da sace-sace.

“Yanzu ya zama a fili cewa Shugaba Tinubu ya gaza sauke babban nauyin da ke kansa na kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa kan yadda masu laifi ke ci gaba da kai hare-hare kan makarantu da sace dalibai, tana mai gargadin cewa bai kamata al’umma su saba da irin wadannan munanan abubuwa ba.

PRP ta ce duk da irin iko da damar da shugaban kasa ke da su, har yanzu gwamnati ba ta nuna ingantaccen mataki da zai kawo karshen matsalar tsaro ba.

Jam’iyyar ta kara da cewa a kasashen da ke bin tsarin dimokuradiyya yadda ya kamata, irin wannan gazawa kan janyo shugabanni su dauki alhakin abin da ya faru.

Saboda haka, PRP ta bukaci ’yan Najeriya su nemi shugabanni su dauki alhakin ayyukansu, tare da matsa lamba kan gwamnatin tarayya domin kawo karshen matsalar rashin tsaro.

Jam’iyyar ta jaddada cewa bai kamata al’umma su jira zuwa zaben shekarar 2027 ba kafin a nemi sauyi, tana mai cewa rayukan ’yan Najeriya na bukatar kariya cikin gaggawa.

Comments (0)
Add Comment