Rana za ta kasance a saitin saman Ka’aba a ranar Babbar Sallah

A wani lamari mai jan hankali da masana suka bayyana a matsayin abin da bai faru ba cikin shekaru 139 da suka gabata, rana za ta kasance a daidai saman dakin Ka’aba a ranar Babbar Sallah ta bana.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin zai faru ne ranar Laraba 27 ga watan Mayun 2026 da misalin ƙarfe 12:18 na rana agogon Makkah, lokacin da rana za ta yi daidai da saman Ka’aba, alkiblar al’ummar Musulmi a faɗin duniya.

Masana sun bayyana cewa wannan yanayi na musamman zai ba Musulmai da ke sassa daban-daban na duniya damar tantance alkiblar da suke fuskanta wajen gudanar da sallah, musamman a yankunan da ke nesa da birnin Makkah.

An bayyana cewa kasancewar rana a daidai saman Ka’aba na faruwa ne sakamakon yadda duniya ke juyawa da kuma tafiyar rana tsakanin yankunan Tropic of Cancer da Tropic of Capricorn.

Lamarin na bana ya zo daidai ne a ranar da alhazai za su fara gudanar da wasu daga cikin manyan ibadun aikin Hajji, ciki har da Jifan Shaidan, yanka hadaya, aski da kuma Dawafin Hajji.

A lokaci guda kuma, Musulmai mazauna gida a sassa daban-daban na duniya za su kasance suna gudanar da bukukuwan Babbar Sallah da yanka layya a ranar 10 ga watan Zul-Hajji.

Masana harkokin falaki sun bayyana wannan rana a matsayin wata muhimmiyar dama ga masu son tabbatar da alkiblar masallatai da gidajensu, domin a daidai lokacin rana za ta nuna sahihin alkiblar Ka’aba kai tsaye.

Comments (0)
Add Comment