Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 23 ga watan Yuni na kowace shekara a matsayin Ranar Zawarawa ta Duniya, domin wayar da kan jama’a game da irin ƙalubale da wahalhalun da matan da suka rasa mazajensu ke fuskanta.
An ƙirƙiri wannan rana ne domin jawo hankali kan matsalolin da zawarawa ke ciki, ciki har da talauci, tauye musu haƙƙoƙinsu, da kuma wariya da ƙyama da suke fuskanta a wasu sassan duniya.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa akwai buƙatar gwamnatoci da al’ummomi su ɗauki matakan kare haƙƙin zawarawa, tare da tabbatar da cewa sun samu damar ilimi, kiwon lafiya, da hanyoyin samun abin dogaro da kai.
Ana kuma amfani da ranar wajen ƙarfafa jama’a da su kawar da al’adun da ke tauye martaba da haƙƙin zawarawa, tare da ba su cikakken goyon baya domin su ci gaba da rayuwa cikin mutunci da walwala.