Rasha ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Moscow bisa harin da aka kaimusu

Tashoshin jiragen sama da dama ne Rasha ta dakatar da zirga-zirga a cikinsu a yau Talata, sakamakon hare-haren da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Ukraine suka kai mata cikin dare, kamar yadda hukumomin Rasha suka sanar

Hukumomin Rasha sun ce kimanin kuramen jirage 19 ne suka kakkaɓo a kusa da babban birnin ƙasar Moscow, inda ake saran shugabannin ƙasashe da dama za su halarci faretin soji da jawabin da shugaba Vladimir Putin zai yi a ranar 9 ga wannan watan, a wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 80 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu.

Kamfanin Dillancin Labaran Rasha ya ruwaito cewar, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta ƙasar ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a tashoshi huɗu da ke birnin Moscow, duk da cewa hakan bai shafi babban filin jirgin sama na Sheremetyevo da ke birnin ba.

Bayaga tashoshin jiragen sama da ke birnin Moscow, matsalar ta shafi wasu birane irinsu Volgograd da kuma Nizhny Novgorod.

A wani sako da magajin garin Mascow Sergei Sobynin ya wallafa a shafinsa na Telegram, ya ce ɓuraɓuzan jiragen da aka harbo sun faɗo a kudancin Moscow, sai dai ya ce basu yi wata ɓarna ba.

Gwamnan jihar Voronezh ya ce sun kama jirage marasa matuƙa 18 da Ukraine ta harbo yankin, sannan shima gwamnan Penza ya bada rahoton kawo 10.

Comments (0)
Add Comment