Rundunar sojin Najeriya ta bukaci ragowar mayakan Boko Haram da su mika wuya su rungumi zaman lafiya.

Rundunar sojin Najeriya ta bukaci ragowar mayakan Boko Haram da su mika wuya su rungumi zaman lafiya.

Babban kwamandan runduna ta 7 ta sojojin Nijeriya, Birgediya Janar A.A. Eyitayo ne ya yi wannan kiran a wajen wani biki da sojoji suka shiryawa ‘yan jarida jiya Lahadi a Maiduguri.

Eyitayo, wanda kuma shi ne kwamandan daya daga cikin rundunar Operation Hadin Kai, ya ce sun fatattaki mayakan a farmakin da sojoji suka kai wanda ya jefa ragowar mayakan da suka tsira cikin rudani.

Ya yi nuni da cewa sojoji basa farinciki dangane da zubar da jini, a saboda haka yana kira ga sauran mayakan su rungumi zaman lafiya su mika wuya.

Hakan a cewarsa zai bawa mayakan damar cin gajiyar shirin canja musu rayuwa da koyar da su sana’o’i domin basu damar gudanar da rayuwa mai amfani a cikin al’umma.

Eyitayo ya yabawa gudunmawar da kafafen yada labarai ke bayawar wajen yaki da masu tayar da kayar baya, inda ya hori ‘yan jarida da su wayar da kan mayaka su gane gaskiya.

Comments (0)
Add Comment