Sabon rahoton Amurka ya yi zargin cewa Fulani mahara na ci gaba da kai munanan hare-hare a Najeriya

Wani sabon rahoton Amurka ya yi zargin cewa Fulani masu ɗauke da makamai na ci gaba da kai hare-hare a sassan Najeriya, musamman yankin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma, inda ake zarginsu da kashe-kashe, satar mutane da ƙona gidaje a yankunan.

Rahoton da BBC Hausa ta fitar ya ce rikicin ya samo asali ne daga matsalolin tsaro, ƙarancin albarkatu, talauci da rikicin addini da ƙabilanci, yana mai ƙiyasin cewa akwai kusan Fulani mahara 30,000 da ke aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Sai dai ƙungiyoyin Fulani ciki har da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria sun musanta zarge-zargen, suna cewa ba su da alaƙa da ta’addanci ko kashe-kashe.

Masanin tsaro Kabiru Adamu ya ce babu wata ƙungiyar Fulani da gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci a ƙarƙashin dokokin ƙasar.

Comments (0)
Add Comment