Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya ce “kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu ba aiki ne na gwamnatin tarayya kawai ba’’, inda a dalilin hakan ne ya ce gwamnatinsa ke ƙoƙarin ganin ta tallafa wajen inganta tsaro a jihar.
Gwamnan ya faɗi haka ne sa’ilin da ya gana da babban sufetan ƴansandan Najeriya Olatunji Disu a Abuja, babban birnin Najeriya.
Sokoto na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, inda ƴan fashin daji ke far wa ƙauyuka suna kashewa tare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
A jawabin da ya yi lokacin da ya gana da babban sufetan, Aliyu ya ce duk da matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a jihar Sokoto, amma jami’an tsaro sun samu nasara a yaƙin da suke yi da matsalar.
Ya bayyana cewa tun bayan zama gwamnan jihar Sokoto, ya sayo tare da raba motocin sintiri guda 200 ga jami’an tsaro domin taimaka musu a yakin da suke yi da matsalar tsaro a yankunan jihar.
“Mun yi hakan ne saboda mun yi amannar cewa tsaron rayuka da dukiyar mutanenmu nauyi ne na kowa da kowa,” a cewar gwamna Aliyu.
Duk da ƙoƙarin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana yi, har yanzu ƴan fashin daji na kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin ƙasar, yayin da ake fama da harin ƴan bindiga a jihohin arewa ta tsakiyar ƙasar.