Tsohon ɗantakarar gwamnn jihar Kogi, Sanata Dino Melaye ya ce ganin yadda gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Bola Tinubu ke cin bashi, yana ganin gwamnatin nan gaba za ta iya cin bashi daga kamfanin hada-hadar kuɗi na intanet wato Opay da moniepoint.
Dino ya bayana haka ne a zantawarsa da tashar ARISE a ranar Litinin, inda ya zargi gwamnatin da jefa ƴan ƙasar nan cikin mawuyacin hali ta hanyar ciyo basussuka da yawa, waɗanda ya ce ba a ganin amfanin su a ƙasa,
Ya tambayi dalilin da yasa Shugaban ƙasa zai nemi bashi na dala biliyan 1.7 daga Bankin Duniya, yayin da Majalisar Dattawa ta riga ta amince da basussuka da suka kai sama da dala biliyan 21, tare da ƙarin wasu da ke kan hanya.
Melaye ya kuma bayyana gwamnatin a matsayin “mafi sakaci a tarihin Najeriya”, yana mai cewa duk da samun kuɗaɗen shiga, har yanzu ana ƙara dogaro da bashi.
Ya yi gargadin cewa, “ba abin mamaki ba idan nan gaba gwamnati ta koma neman bashi daga Opay da Moniepoint.”