Sanata Ningi Ya Ce Abin da Za Mu Ji Na Gaba Shi Ne An Sace Akpabio

Wani dan majalissar dattawa mai wakiltar Mazabar Ningi/Warji a Jihar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Abdul Ningi, a ranar Laraba ya yi tambaya kan dalilin da ya sa ake zargin an ware Majalissar Tarayya daga tattaunawar diflomasiyya da ta ba da damar kai hare-haren jiragen yakin sojojin Amurka a Jihar Sokoto.

Da yake magana yayin muhawara kan hare-haren jiragen yakin da rahotanni suka ce sun kashe wasu ‘yan ta’adda a Sokoto a daren Kirsimeti, dan majalissar ya ce aikin sojan ya saba wa Yarjejeniyar Majalissar Dinkin Duniya (UN).

Ya bayyana damuwa cewa idan aka bar irin wadannan hare-haren su na gudana a Najeriya ba tare da bin ka’idoji ba, wasu kasashe za su iya daukar mataki a kan kasar.

Ya kuma lura cewa idan Majalissar Tarayya ta amince da faruwar hakan, shugabannin Majalissar Dattawa, ciki har da Shugaban Majalissar, Godswill Akpabio, na iya fuskantar hari a nan gaba idan aka zartar da wasu dokoki.

Ya ce, “Idan muka bar wannan lamari ya ci gaba haka nan, ba gwamnatin Amurka kadai ba ce ke da karfin soja a doron kasa. Idan Rasha ta nemi wani abu muka ki, za ta iya daukar mataki. Idan muka hana sojojin UN biyan bukatunsu, za su iya daukar mataki. Jamusawa, Faransawa, su ma za su iya daukar mataki.

“Mai girma Shugaba, idan muka bar wannan ya faru kuma muka zartar da doka a nan da za ta cutar da wata kasa mai karfi, abin da za mu ji na gaba shi ne an sace Shugaba Akpabio an tafi da shi.”

Comments (0)
Add Comment