Sanatoci Sun Kai Ziyara Rijiyar Farko Ta Man Fetur A Najeriya Da Ke Oloibiri

Shugaban Kwamitin Albarkatun Man Fetur na Majalisar Dattijai (Downstream), Sanata Muhammad Kawu Sumaila, tare da sauran mambobin kwamitin, sun kai ziyara zuwa rijiyar farko ta man fetur da aka haƙa a Najeriya.

Tawagar ta haɗa da tsoffin gwamnonin jihohin Plateau da Sokoto, Sanata Simon Lalong da Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da kuma Sanata Abdul Ningi, tare da wasu mambobin kwamitin.

Sun kai ziyarar ne zuwa garin Oloibiri da ke jihar Bayelsa, inda aka fara gano albarkatun man fetur a Najeriya a shekarar 1956, lamarin da ya zama muhimmin tarihi a fannin tattalin arzikin ƙasar.

Ziyarar ta kasance wani ɓangare na ayyukan sa ido da tantance harkokin man fetur, tare da duba muhimmancin wurin da ya kasance tushen fara haƙo man fetur a Najeriya. Tawagar ta kuma jaddada buƙatar kiyaye tarihin Oloibiri da kuma samar da ƙarin ci gaba ga al’ummomin yankin da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin masana’antar man fetur ta ƙasar.

Comments (0)
Add Comment