SARKIN DUTSE YA KADDAMAR DA KWAMITIN BINCIKE KAN HAKIMIN FAGAM

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dakta Muhammadu Hamim Nuhu Sanusi, ya kaddamar da wani kwamitin bincike domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa Hakimin Fagam, Katikan Dutse Alhaji Auwalu Adamu.

Sarkin ya samu wakilcin Galadiman Dutse, Alhaji Basiru Muhammadu Sanusi, wanda ya bukaci mambobin kwamitin su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rikon amana.

Kwamitin na karkashin jagorancin Alhaji Mustapha Aminu Wamban Dutse, tare da sauran manyan masu fada a ji, wakilan hukumomin tsaro da kuma ‘yan jarida.

Daga cikin zarge-zargen da ake yi wa Hakimin akwai hana Fulani mallakar gonakin iyayensu sai sun saya, da kuma sayar da burtalai da wuraren kiwo ga manoma, lamarin da ake zargin ya janyo karancin filayen kiwo a yankin.

Comments (0)
Add Comment