Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Matsalar Tsaro A Najeriya

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sake yin kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen magance matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, musamman yankin Arewa.

Sarkin ya tunatar da cewa tun a shekarar 2020, ya taba yin gargadi cewa ’yan bindiga suna shiga kasuwanni a Arewa suna sayayya da makamai a bayyane, amma gwamnati ta kasa daukar matakin da ya dace.

A cewar rahoton Amnesty International, sama da mutane 10,000 aka kashe tsakanin 2023 da 2025 a hare-haren ’yan bindiga da ta’addanci a jihohin Benue, Plateau, Katsina, Kebbi, Sokoto, Edo da Zamfara.

Rahoton ya kuma bayyana cewa a Zamfara, ’yan bindiga suna da iko a kan kauyuka 725 inda suke amfani da zinariya don siyan makamai daga ƙasashen waje ta Niger da Mali.

A makonni biyu da suka gabata, Boko Haram da ISWAP sun kai harin da jirgi maras matuki a sansanonin soja na Borno da Yobe, inda sojoji suka mayar da martani suka kashe fiye da 50 daga cikinsu. Duk da haka, hare-hare na ci gaba kuma manoma suna fuskantar hare-hare da rasa rayuka, wanda ke haifar da karuwar yunwa a ƙasar.

A halin yanzu, ’yan sanda a Najeriyaadadinsu bai isa ba. A cikin jami’an 371,800, kusan 150,000 suna yi wa ’yan siyasa da masu kudi gadin kai, suna barin talakawa ba tare da kariya ba. Wannan ya sa rabon jami’in ’yan sanda da jama’a ya zama 1:650, maimakon 1:450 da Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta tsara.

Comments (0)
Add Comment