Masarautar Saudiyya ta fara rabon tallafin abinci ga al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a Najeriya karkashin Shirin Tallafin Abinci na shekarar 2026, wanda zai amfanar da sama da mutum 145,000 a jihohi biyar da matsalolin rashin tsaro, ƙaura da sauran matsalolin jin kai suka fi shafa.
Shirin, wanda Cibiyar Agajin Jin Kai ta Sarki Salman (KSrelief) ke aiwatarwa tare da haɗin gwiwar kungiyar Ihsan for Relief and Development, zai raba tan 1,400 na kayan abinci ga iyalai 24,700 a jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Kano da Zamfara.
Jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin Masarautar na tallafa wa al’ummomin da ke fama da matsalolin jin kai a duniya, musamman waɗanda rikice-rikice da rashin tsaro suka shafa.
Ya bayyana cewa kowane kunshin kayan abinci na ɗauke da muhimman kayan masarufi da za su taimaka wa iyalai masu rauni wajen samun abinci mai gina jiki.
Shugaban kungiyar Ihsan for Relief and Development, Dr. Abdullahi Saleh, ya yabawa gwamnatin Saudiyya bisa wannan tallafi, yana mai cewa zai taimaka wajen rage wahalhalun da dubban iyalai ke fuskanta a yankunan da matsalolin tsaro da ƙaura suka yi kamari.
An bayyana cewa shirin zai gudana cikin matakai daban-daban domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda suka fi buƙata a jihohin da aka zaɓa.