Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Alƙali Abubakar Zaria, ya bayyana shirinsu na kafa wata ƙungiya da za ta samar da bulalai sama da 50,000 domin ladabtar da mutanen da ke karɓar kuɗi, taliya ko wasu kayayyaki a madadin ƙuri’arsu yayin zaɓe.
Malamin ya ce sayar da ƙuri’a na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa matsalolin cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro a Najeriya, yana mai cewa al’umma su ne ke da alhakin zaɓar shugabanni nagari.
Ya yi kira ga jama’a da su guji bai wa ‘yan siyasa damar sayen ƙuri’unsu, yana mai jaddada cewa karɓar kuɗi ko kayan tallafi domin zaɓe na da illa ga makomar ƙasa da jin daɗin al’umma.