Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Karbi Ragamar Shugabancin Kasarnan

A yau Litinin 29 ga watan Mayu, an rantsar da Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa na 7.

Ana  gudanar da bikin rantsar da sabuwar gwamnatin ne a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Gwamnatin Tinubu za ta kasance ta 17 a kasar tun bayan da Birtaniya ta mika wa Najeriya mulkin kasar bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960.

Sawaba ta ruwaito cewa, shugabancin Tinubu zai kasance karo na biyar tun bayan da Najeriya ta koma kan turbar dimokradiyya a watan a Mayun 1999, bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya jagoranci kasar tsakanin (1999-2007),sai Marigayi Umar Musa Yar’Adua da ya jagoranci kasar (2007-May 2010), Goodluck Jonathan (Mayu 2010-2015) sai Muhammadu Buhari (2015-2023).

Tinubu zai karbi ragamar mulki daga hannun Buhari, wanda ya kammala wa’adinsa biyu na shekaru 8 a yau.

Tsohon gwamnan na jihar Legas zai karbi ragamar shugabancin kasar ne tare da zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, kuma tsohon gwamnan jihar Borno.

Haka zalika, za a rantsar da gwamnoni 28 a fadin shiyyoyin shida na kasarnan, ciki har da tsofaffin gwamnoni goma da aka sake zabar su a karo na biyu.

Comments (0)
Add Comment