Shugaba Buhari Ya Magance Matsalar Rashin Tsaro, Sake Fasalin Tattalin Arziki Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Ministoci da masu taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai sun ce za’a ke tunawa da gwamnatin Buhari bisa bullo da shirye-shiryen da suka sauya salon mulki a kasar nan.

Mataimakan sun bayyana ra’ayinsu ne a cikin wani shiri na tsawon mintuna 55 da ma’aikatar yada labarai ta fadar gwamnatin tarayya ta shirya kuma aka watsa a gidan talabijin na kasar a jiya.

Wadanda suka fito a cikin shirin sun hada da: Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, Ministan Babban Birnin Tarayya, Mohammed Musa Bello, Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyema, Karamin Ministan Muhalli Sharon Ikeazor da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan yada Labarai Femi Adesina; Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu.

Sun yi jawabi a bangarori daban-daban na irin ayyukan da gwamnatin shugaban kasa Muhamadu Buhari ta yi.

A yayin da Shehu ya yi karin haske kan yadda gwamnatin ta shafe shekaru takwas ta na mulki, yace Shugaba Buhari ya magance matsalar rashin tsaro, sake fasalin tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa cikin shekaru 8 da suka gabata.

Comments (0)
Add Comment