Shugaba Tinubu bai taba umarta na da kama ko tsoratar da ‘yan jarida ba ko da kuwa suna suka – Mohammed Idris

Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai taba umartansa da ya kama ko tsoratar da ‘yan jarida ba, ko da kuwa suna suka.

A wata ganawa da Kungiyar Editocin Najeriya, Idris ya jaddada cewa wannan gwamnati na mutunta ‘yancin fadin albarkacin baki da dimokuradiyya.

Ya kuma bayyana shirin kafa cibiyar koyar da karatun kafofin labarai da hadin gwiwar UNESCO.

Za a kafa cibiyar ne a Jami’ar National Open University don yaki da labaran karya da yada jita-jita. Ministan ya bukaci ‘yan jarida da su rika rike gwamnati da alhaki cikin mutunci.

Comments (0)
Add Comment