Shugaban ƙaramar hukumar Hadejia ya sha alwashin inganta harkokin ilimi a yankin

Shugaban ƙaramar hukumar Hadejia, Alhaji Ahmed Abba Ari, ya sha alwashin inganta harkokin ilimi a yankin, yayin da ya kaddamar da rabon kayan koyarwa da magungunan farko ga makarantun firamare da na sakandare a garin Hadejia.

A cikin jawabin sa, ya ce wannan mataki na daga cikin hanyoyin da hukumar ke amfani da su wajen aiwatar da manufofin gwamnati na tabbatar da ingantaccen ilimi da kula da lafiyar ɗalibai.

A jawabin nasa, Sakataren Ilimi Alhaji Musa Garba ya ce makarantun firamare 53 za su samu takardun shaidar ƙare karatu da littattafan tsare-tsaren koyarwa, yayin da makarantun sakandare 22 za su karɓi magunguna da kayan rubutu ga ɗalibai mata 950.

Shugaban kwamitin kula da makarantu Imam Aminu Hassan ya nuna godiya bisa wannan tallafi, tare da alƙawarin amfani da kayayyakin da suka samu ta hanya mai kyau don amfanin ilimi a yankin.

Comments (0)
Add Comment