Shugaban ƙasa ya ce makomar Najeriya na hannun matasa, ya bukace su da su daina barin Najeriya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga matasan Najeriya da kada su yi watsi da ƙasarsu ta hanyar yin hijira zuwa ƙasashen waje, yana mai cewa Najeriya ita ce gidansu kuma makomarsu.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya yi wa al’umma a bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 2026, inda ya bukaci matasa su ba da gudummawarsu wajen gina ƙasa maimakon neman mafita a ƙetare.

“Ga matasanmu, Najeriya ita ce gidanku kuma makomarku. Ku yi gini a nan, ku yi aiki a nan, ku ƙirƙiri fasaha a nan, kuma ku kada kuri’a a nan. Manyan ƙasashe sun samu ci gaba ne saboda mutanen da suka zauna suka magance matsalolinsu, ba waɗanda suka gudu suka bar su ba,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya bayyana cewa yayin da tsofaffin ƙarnuka suka yi gwagwarmayar samun ‘yancin kai da tabbatar da dimokuraɗiyya, babban aikin da ke gaban matasan yau shi ne tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta samar da walwalar tattalin arziki da damammaki ga jama’a.

Ya ce dimokuraɗiyya ba za ta yi tasiri ba idan al’umma ba sa ganin amfaninta a rayuwarsu ta yau da kullum, yana mai cewa gwamnatin sa ta mayar da hankali wajen samar da damammakin aiki da ci gaba ga matasa.

Shugaban ya kuma bukaci matasa da su guji yanke kauna, rarrabuwar kawuna da rashin fata mai kyau, abubuwan da ya ce suna ƙara ruruta sha’awar yin abin da aka fi sani da “Japa”, wato hijira zuwa ƙasashen waje domin neman rayuwa mai kyau.

Sai dai duk da wannan kira, rahotanni sun nuna cewa dubban matasan Najeriya na ci gaba da barin ƙasar kowace shekara domin neman ingantacciyar rayuwa, lamarin da ya shafi fannoni da dama ciki har da lafiya, ilimi, fasaha da aikin injiniya.

Masana na ganin cewa ci gaba da ficewar ƙwararru daga Najeriya na haifar da gibin ma’aikata a muhimman sassa, duk da cewa kuɗaɗen da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida na taimakawa tattalin arzikin ƙasar.

Tinubu ya kammala da kira ga matasa da su kasance masu kyakkyawan fata tare da haɗa kai wajen magance matsalolin Najeriya daga cikin gida.

Comments (0)
Add Comment