An samu tashin hankali a Jihar Ondo da ke kudancin Najeriya, bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ya rikide zuwa rikici, inda wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai hari tare da raunata mutane da dama, ciki har da shugaban jam’iyyar na jihar da kuma wani kwamishina.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a sakatariyar jam’iyyar da ke birnin Akure, ƙasa da sa’o’i 24 kafin a gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar a matakin unguwanni 203 a faɗin jihar.
Wata shaidar gani da ido, Yetunde Adeyanju, ta ce maharan sun shigo dauke da makamai, suna ikirarin cewa suna goyon bayan gwamnan jihar. Ta ce sun yi barazanar cewa ba za su amince da gudanar da zaɓen ba, tare da gargadin cewa duk wanda ya yi magana a kan zaɓen zai fuskanci mummunan sakamako.
Wata shaidar ta daban ta tabbatar da cewa an lakada wa shugabannin jam’iyyar da dama duka, ciki har da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Ade Adetimehin, da wani jami’i a Hukumar Raya Yankin Neja Delta, Otito Atikase, da kuma tsohon kwamishinan wasanni, Saka Yusuf-Ogunleye. An ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.
Da yake magana kan lamarin, shugaban jam’iyyar na jihar, Ade Adetimehin, ya ce ‘yan daban sun kai harin ne domin tarwatsa taron. Ya ce sun buge shi tare da jan sa a ƙasa, sannan suka kwace wayoyinsa guda biyu, kuɗi da kuma agogonsa.
Sai dai kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Idowu Ajanaku, ya musanta zargin cewa gwamnan jihar na da hannu a harin, yana mai cewa zargin ba shi da tushe kuma yaudara ce. Ya ce gwamnan bai san da taron ba kuma ba zai amince da duk wani nau’in tashin hankali ko tsoratar da jama’a ba.
A nasa bangaren, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ‘yan sanda sun samu kiran gaggawa kuma sun tura jami’ansu zuwa wurin domin shawo kan rikicin.
Ya ƙara da cewa an dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a harin.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da muhimmin zaɓen shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa, wanda ke da tasiri wajen tsara makomar jam’iyyar a jihar Ondo.