Shugaban jami’ar Jos (UniJos), Farfesa Ishaya Tanko, ya buƙaci ɗalibai da ma’aikatan jami’ar su ƙara taka-tsantsan sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan hare-hare da kashe-kashe a wasu sassan jihar filato.
Umarnin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tashin hankali a tsakanin al’ummah a faɗin jihar, lamarin da ya ƙara jefa fargaba a birnin Jos, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin dawo da zaman lafiya.
Rahotanni na nuna cewa an tura jami’an tsaro, ciki har da sojoji da ‘yan sanda, zuwa muhimman wurare a babban birnin jihar domin kare rayuka da dukiyoyi.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin mai kula da Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Emmanuel Madugu, ya sanya wa hannu, mahukuntan jami’ar sun shawarci ɗalibai da ma’aikata da su guji zirga-zirgar da ba ta da muhimmanci, musamman da sanyin safiya.
Sanarwar ta kuma buƙaci duk wani mamba na jami’ar da ya lura da wata alamar barazana ga zaman lafiya ya gaggauta sanar da Sashen Tsaro na jami’ar.
Mahukuntan jami’ar sun tabbatar wa da al’ummar makarantar cewa suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da cikakken tsaro ga rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga kowa da ya kasance cikin shiri yayin da hukumomi ke ƙoƙarin tabbatar da kwanciyar hankali.