Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta bullo da wani sabon tsari domin dakile yawaitar sauya sheƙa da ‘ya’yanta ke yi bayan sun samu nasara a zaɓe.
A ƙarƙashin wannan sabon mataki, duk ‘yan takarar gwamna da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa na jam’iyyar, ciki har da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, za su sanya takardun alƙawari (indemnity forms) da ke nuna cewa idan suka fice daga jam’iyyar bayan sun ci zaɓe a ƙarƙashin tutarta, za su amince su bar kujerun da suka samu.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da biyayya ga jam’iyya da kuma kare kuri’un da al’umma suka ba wa ‘yan takara a ƙarƙashin tutar NDC.