Sojin ruwan ƙasashen Koriya ta Kudu da Amurka da Japan na gudanar da atisayen kwanaki biyu.

Sojin ruwan ƙasashen Koriya ta Kudu da Amurka da Japan na gudanar da atisayen kwanaki biyu, domin inganta aikinsu.
A wani mataki na tauna tsakuwa kan barazanar hare-haren makamai masu linzami na Koriya ta Arewa.
Manufar Tisayen shi ne faɗaɗa ikonsu da horon da zai ba su damar kare teku kan hare-haren makaman nukiliya na ƙarƙashin teku da Arewar ta fara yi a baya-bayan nan.
Za su samu horo kan yadda za su iya gano makamin nukiliya da zarar an sanya shi cikin teku.
Inda za a sanya wasu motocin teku na musamman a matsayin kan-da-garki.
Wannan dai shine karon farko da kasashen ke gudanar makamancin atisayen cikin shekaru 5, domin tauna tsakuwa kan barazanar gwajin wasu makamai da Korea ta arewa ta soma.

Comments (0)
Add Comment