Sojoji Sun Fatattaki ’Yan Bindiga, Sun Kwato Dabbobi 529 A Katsina

An yi musayar wuta a Jihar Katsina inda dakarun Sojin Najeriya suka fafata da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a Ƙaramar Hukumar Kafur,  samu an kuma samu nasarar kwato dabbobi 529 da aka sace.

Rundunar Sojin ta ce dakarunta na Brigade ta 17 da ke Katsina ne suka gudanar da wannan aiki, ƙarƙashin sansanin Forward Operation Base (FOB) Malumfashi, bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan ’yan bindiga a yankin Kasuwan Sabo.

Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Abayomi Adisa, ya bayyana cewa aikin da aka gudanar a ranar 7 ga Fabrairu, 2026, ya mayar da hankali ne kan wasu ’yan ta’adda da ake zargin sun shigo jihar daga maƙwabciyar ta Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa waɗannan ’yan bindiga na ƙarƙashin jagorancin Idi Abasu Aiki, wanda ake zargin ƙanin shahararren jagoran ’yan bindiga ne, Ado Aliero.

Da zarar sun hangi dakarun na tunkararsu, sai ’yan bindigar su buɗe wuta, lamarin da ya haifar da musayar wuta, amma dakarun sun mayar da martani cikin kwarewa, hakan ya tilasta wa maharan tserewa zuwa cikin daji tare da barin wasu daga cikin dabbobin da suka sace.

Rundunar ta ce babu wani soja da ya jikkata, duk da cewa shanu 14 sun mutu yayin musayar wutar, kuma an miƙa dabbobin da aka kwato ga hukumomi domin tantancewa da mayar da su ga masu su, yayin da manyan hafsoshin soja suka yabawa dakarun bisa jajircewar da suka nuna.

Comments (0)
Add Comment