A cigaba da yaki da matsalar tsaro a Katsina, sojojin Najeriya sun yi nasarar kawar da ’yan fashi bakwai a Karamar Hukumar Kankara.
An gudanar da samamen ne bisa bayanan sirri da aka samu cewa ’yan fashin sun kai hari ƙauyen Baba. Samamen ya ɗauki fiye da awa biyu, inda aka kuma kwace babura huɗu. Wannan nasara ta zo ne bayan makonni kaɗan da aka yi mummunan hari a wani masallaci, wanda ya yi sanadin salwantar rayukan mutane kusan 50.