Sojojin Najeriya Sun Kwato Gawar Kwamanda da Wasu Sojoji Shida da Boko Haram Suka Kashe a Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kwato gawar wani kwamandan soja, wani manjo da kuma wasu sojoji shida da ’yan ta’addan Boko Haram suka kashe a yankin Damasak na Jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan sojojin sun faɗa tarkon ’yan ta’adda a yayin da suke kan hanyar kai farmaki zuwa wani babban sansanin Boko Haram da ke tsakanin Damasak da Geidam.

Da farko an yi zaton cewa kwamandan na daga cikin waɗanda aka kama da rai, amma daga bisani jami’an tsaro suka tabbatar da cewa shi da sauran sojojin an kashe su, tare da wasu mambobin Civilian Joint Task Force (CJTF) biyu.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa an samu gawawwakin ne a ranar Laraba bayan gumurzu mai tsanani tsakanin sojoji da ’yan ta’adda, tare da goyon bayan jiragen yaƙi.

Majiyar ta ƙara da cewa ’yan Boko Haram sun yi yunƙurin kai wa sojojin hari yayin aikin kwato gawawwakin, amma bayan samun ƙarin dakaru da tallafin sama, an fatattake su.

Daga bisani an ɗauko gawawwakin ta jirgi zuwa Maiduguri domin ci gaba da matakan da suka dace.

Comments (0)
Add Comment