Sojojin Najeriya Sun Kwato Litar Danyen Mai 1.06M Daga Haramtattun Wurare 41 Na Tace Danyen Mai

Hedikwatar tsaron ta ce sojojin Najeriya sun lalata haramtattun wurare 41 na tace danyen man fetur tare da kwato sama da lita miliyan 1.06 na danyen man a cikin makonni biyu da suka gabata.
Darakta mai kula da harkokin yada labaran tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka jiya a Abuja, yayin taron manema labarai na mako biyu kan ayyukan rundunar sojan.
Ya kara da cewa, injinan dafa mai 156, da tankunan ajiya 189, da ramuka 12 da kuma kwale-kwalen katako 15 sojojin suka lalata.
Musa Danmadami ya ce, baya ga danyen mai, an kama litar man gas dubu 13 da 500 da man fetur lita dubu 8 da 500 da motoci 6 da wasu mutane 18 da ake zargi.
A wani batun kuma, Musa Danmadami ya ce sojojin a ranar 25 ga watan Afrilu, sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne su biyar da suka kai wa ‘yan banga hari a hanyar Iyara da ke karamar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta.
Ya ce an kwato bindigogi biyu, wukake biyu, adduna biyu da babur daya daga hannun wadanda ake zargin.

Comments (0)
Add Comment