Sudan ta umurci ƴan gudun hijira su fice daga makarantun da suke mafaka

A yau ne wa’adin kwana biyar da hukumomin Sudan suka bai wa dubban ’yan gudun hijira da ke mafaka a makarantun gwamnati a El-Obeid, babban birnin jihar Kordofan ta Arewa, ya cika.

Rahoton gidan jaridar Darfur24 mai zaman kanta ya ce an bai wa ’yan gudun hijirar umarni duk da babu tsare-tsare na musu matsuguni na madadin makarantun da suke kwana.

Birnin da sojojin Sudan ke riƙe da shi na ɗauke da sama da ’yan gudun hijira 700,000 da aka raba da muhallansu sakamakon tashin hankali da dakarun RSF a yankin Kordofan.

Hukumar ilimi ta jihar ta ce makarantu za su buɗe a ranar 17 ga watan Agusta, lamarin da ake fargabar zai kara tsananta halin da ’yan gudun hijirar ke ciki.

Comments (0)
Add Comment