Sufeto Janar na ’Yan Sanda Ya Ɗaga Matsayin Ƙananan Jami’ai 17,952 a Faɗin Najeriya

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya amince da ɗaga matsayin jami’an ‘yan sanda 17,952 a faɗin ƙasar nan, a wani mataki da ke nuna ƙoƙarin rundunar wajen ƙarfafa gwiwa da inganta walwalar jami’anta.

Mai magana da yawun rundunar, Anthony Placid, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin manufofin rundunar na ƙara wa jami’ai ƙwarin gwiwa, tare da karrama sadaukarwa da jajircewar da suke nunawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasa.

Ya ce karin matsayin zai taimaka wajen ƙarfafa himma da kwazo a tsakanin jami’an rundunar, tare da nuna cewa ana yaba wa ƙoƙarinsu da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Sufeto Janar ɗin ya kuma buƙaci jami’an da aka ƙara wa matsayi da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya, ƙwarewa da biyayya ga doka, yana mai jaddada muhimmancin kare haƙƙin jama’a da bin ƙa’idojin aikin ɗan sanda a kowane lokaci.

Matakin ya samu karɓuwa daga jami’ai da dama, inda ake ganin zai ƙara wa rundunar kuzari wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da kuma inganta ayyukan tabbatar da doka da oda a faɗin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment