Sule Lamido Na Neman Shugabancin Jami’yyar PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Sule Lamido, ya bayyana aniyarsa ta nema kujerar shugabancin jam’iyyar PDP.

Lamido ya sanar da hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce zai sayI fam ɗin takarar shugabancin jam’iyyar a yau Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 11:00 na safe, a Wadata Plaza, hedikwatar PDP da ke Abuja.

A cewarsa, “Ba gudu, ba ja da baya. Yau Litinin, 27 ga watan Oktoba, da ƙarfe 11 na safe zan siya fam ɗin takarar shugabancin jam’iyyar PDP.”

Tsohon gwamnan, wanda ke ɗaya daga cikin tushen ginshiƙan jam’iyyar tun daga kafuwarta, ya ce aniyarsa ita ce dawo da martabar PDP, tare da haɗa kan ‘ya’yan jam’iyyar domin farfaɗo da ƙarfinta kafin babban zaɓen 2027.

Lamido ya kara da cewa ƙudurinsa na gina dimokuraɗiyya da sabunta jam’iyyar ba zai tsaya ba, domin, a cewarsa, lokaci ya yi da PDP za ta komawa tsohon darajarta a siyasar Najeriya.

Comments (0)
Add Comment