Taimako mu ke bukata ba dokar ta-baci ba — Gwamna Alia

A yayin da kashe-kashen mutane ke ci gaba da karuwa a jihar Benue, Gwamnan jihar, Reverend Father Hyacinth Alia, ya bayyana cewa abinda mutanen Benue ke bukata shine cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya, ba ayyana dokar ta-baci ba.

Da yake magana a shirin “The Morning Show” na Arise a ranar Laraba, Gwamna Alia ya ce matsalar rashin tsaro a jihar Benue ba ta fi karfinsa ba, sai dai yana bukatar taimakon Gwamnatin Tarayya domin shawo kan rikicin.

Ya ce gwamnatinsa tana da karfin magance kashe-kashen da ake yi a jihar, amma yana bukatar karin goyon baya domin korar makiyayan da ke kai hare-hare a cikin al’ummomin jihar Benue.

Ya ce, “Abinda muke bukata yanzu taimakon gaggawa ne. Muna bukatar cikakken goyon baya. Gwamnatin tarayya na tare da mu. Sun turo tankokin yaki guda biyu. Hakan ya sauya yanayinmu. Labarin ya fi kyau yanzu, amma abinda ya kamata mu yi shine dawo da mutanenmu gida, mu kori mamayen da ke dauke da makamai, wadanda har ba su ma iya harsunan Najeriya da muke amfani da su ba. Ya kamata su koma inda suka fito, su bar mu manoma mu koma gonakin kakanninmu. Babu bukatar ayyana wata dokar ta-baci a nan.”

Comments (0)
Add Comment