Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto

Wani sabon rahoto da hukumar ƙididdiga ta jihar Sokoto ta fitar ya nuna cewa an samu raguwar talauci a jihar, inda ya sauka daga kaso 91 zuwa kaso 41 cikin ’yan shekarun nan.

Rahoton ya bayyana cewa wannan ci gaba na da alaƙa da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen inganta rayuwar al’ummar karkara, musamman ta hanyar zuba jari a fannin samar da kayayyakin more rayuwa.

A cewar rahoton, a shekarar 2026, gwamnatin jihar ta ware kaso 70 na kasafin kuɗinta domin ayyukan raya ƙasa, wanda hakan ya taimaka wajen samar da sauƙin rayuwa ga jama’a da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Sai dai rahoton ya nuna cewa har yanzu akwai ƙalubale, musamman a wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro. An ambaci ƙananan hukumomi kamar Tangaza da Binji a matsayin wuraren da talauci ya fi ƙamari sakamakon matsalolin tsaro da ke addabar yankunan.

Rahoton ya kuma nuna alaƙa mai ƙarfi tsakanin talauci da rashin tsaro, inda ya bayyana cewa rashin zaman lafiya na hana cigaban tattalin arziƙi da kuma ƙara tsananta talauci a wasu sassan jihar.

A shekarar 2022 dai, rahotanni sun nuna cewa talauci ya kai kaso 91 a jihar Sokoto, abin da ya sanya ta cikin jihohin da suka fi fama da talauci a Najeriya.

Sai dai sabon rahoton ya nuna cewa matakan da aka ɗauka na ci gaba da samar da ababen more rayuwa da kuma tallafawa al’umma sun fara haifar da da mai ido.

Comments (0)
Add Comment