Tashin Abin Fashewa Ya Jikkata Mutum Ɗaya A Legas

Wani mutum ya jikkata bayan wani abin fashewa da aka dasa a ƙarƙashin motarsa kirar Toyota Sienna ya tashi a yankin Oke Mushin da ke Jihar Legas da safiyar Litinin.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Tijani Fatai, ya ce binciken farko ya nuna cewa an dasa na’urar fashewar ne a ƙarƙashin motar, kuma ta tashi ne jim kaɗan bayan an kunna ta.

An garzaya da wanda ya jikkata zuwa asibiti domin yi masa magani, yayin da jami’an EOD suka kwato ragowar abin fashewar tare da fara bincike kan lamarin.

Comments (0)
Add Comment