Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ɗaga matsayin fitaccen ɗan jarida, Abdulaziz Abdulaziz, zuwa muƙaminTinubu Ya Ɗaga Darajar Abdulaziz Abdulaziz Zuwa Babban Mai Ba Shi Shawara Kan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kan Jama’a wato Senior Special Assistant to the President on Media and Public Enlightenment (SSA MPE).
Tun da farko, Abdulaziz Abdulaziz ya riƙe muƙamin Senior Special Assistant on Print Media, kafin a sake fasalin ofishinsa tare da ƙara masa girma da faɗaɗa aikinsa zuwa harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a.
Sabon muƙamin na nuna ƙarin amincewa da gogewa da ƙwarewar da Abdulaziz Abdulaziz ya nuna a fannin aikin jarida da kuma aikin yaɗa manufofi da shirye-shiryen gwamnatin tarayya.