Tinubu Ya Amince Najeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taron Shugabannin Hukumomin Ƙwallon Ƙafa Na Afirka

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince Najeriya za ta ɗauki nauyin taron shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na Afirka da ke ƙarƙashin Confederation of African Football, wanda ake sa ran gudanarwa a wannan shekara.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da shugaban CAF, Patrice Motsepe, tare da tawagarsa a birnin Nairobi, inda suka tattauna kan ci gaban harkokin ƙwallon ƙafa da hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka.

Rahotanni sun nuna cewa taron zai haɗa shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa daga sassa daban-daban na nahiyar domin tattauna batutuwan ci gaba, gudanarwa da kuma bunƙasa wasanni a Afirka.

Matakin da Najeriya ta ɗauka na nuna ƙara himma wajen tallafa wa harkokin wasanni da ci gaban ƙwallon ƙafa a nahiyar, tare da sa ran taron zai ƙara ɗaukaka martabar wasannin Afirka a idon duniya.

Comments (0)
Add Comment