Tinubu Ya Jajanta Wa El-Rufai Kan Rasuwar Mahaifiyarsa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga tsohon gwamnan jihar Kaduna da iyalansa, Mallam Nasir El-Rufai game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma da ta rasu ranar Juma’a.

Cikin saƙon ta’aziyyar da ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayiyar a matsayin wadda ta cimma nasara a rayuwa wajen renon ƴaƴa da jikokin da suka taimaka wajen gina Najeriya.

“Ina miƙa ta’aziyya ga El-Rufai da iyalansa kan wannan rashi, a matsayin wanda ni ma na rasa mahaifiyata na sa irin raɗaɗin da rashin mahaifiya ke da shi”, in ji Tinubu.

Ya ce rasuwar mahaifiya na da ciwo fiye da komai, don haka ya yi addu’ar haƙurƙurtar da iyalanta game da rashinta.

Hajiya Umma ta rasu en ranar Juma’a da dad

Comments (0)
Add Comment