Tinubu ya kafa kamfanin zuba jari da raya yankin Kudu maso Gabas tare da zuba jarin farko na Naira Biliyan 150 don soma aiki

Tinubu ya amince da kafa kamfanin zuba jari da raya yankin Kudu maso Gabas tare da zuba jarin farko na Naira Biliyan 150bn a kamfanin don soma aiki.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa kamfanin raya yankin Kudu maso Gabas wato South-East Investment Company tare da zuba masa jarin farko na Naira biliyan 150bn domin soma aiki.

Kamfanin zai kasance karkashin hukumar raya yankin Kudu maso Gabas ne wato South East Development Commission (SEDC), kuma an samar da kamfanin ne domin haɓaka masana’antu da jawo masu zuba jari da yan kasuwa a yankin Kudu Maso Gabas. Majiyar A Yau ta ruwaito Gwamnati na cewa an shirya kamfanin ya rika samar da kuɗi ta hanyar kasuwanci da sayar da hannayen jari ba tare da dogaro da kasafin gwamnatin tarayya ba.

Comments (0)
Add Comment