Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa, Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB).
Aina mai shekaru 39 ya maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede, wanda wa’adinsa a matsayin shugaban hukumar zai ƙare ranar 31 ga watan Yulin 2026.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, inda ya bayyana sabon shugaban JAMB a matsayin ƙwararren masani mai gogewa a harkokin gudanar da jarrabawa, fasahar intanet da kuma sauye-sauyen da suka shafi ci gaban al’umma.
Sanarwar ta ce gwamnatin Tinubu na sa ran sabon shugaban zai kawo sababbin tsare-tsare da dabaru domin ƙarfafa sahihanci, inganci da kuma ci gaban tsarin jarrabawar shiga jami’o’i a Najeriya.
Farfesa Aina na daga cikin matasan ƙwararrun masana da suka yi fice a harkokin ilimi da fasaha, lamarin da ya sa gwamnatin tarayya ta nuna kwarin gwiwa kan jagorancinsa a hukumar.
Naɗin nasa na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan gyaran tsarin jarrabawa da kuma bunƙasa amfani da fasaha wajen gudanar da ayyukan ilimi a ƙasar.