Tinubu ya sanar da ceto mutum 38 da aka sace a cocin jihar Kwara

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da ceto masu ibada 38 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku, jihar Kwara.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaban ya ce:

“Godiya ga jami’an tsaronmu a ‘yan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Eruku na jihar Kwara.” Duk da haka, bai bayyana ƙarin bayani kan yadda aka gudanar da ceto ba.

Haka zalika, Tinubu ya tabbatar da ceton ɗalibai 51 daga cikin 315 da aka sace a jihar Neja. Shugaban ya ce:

“Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a ƙasa baki ɗaya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan ke faruwa. Haka nan, ina mai farin ciki cewa an gano 51 daga cikin ɗaliban makarantar Catholic School ta jihar Neja”.

A baya, ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya ta bayyana cewa ɗaliban sun samu tsere daga hannun masu garkuwa tsakanin Juma’a da Asabar, bayan da aka sace su ranar Alhamis da dare.

Comments (0)
Add Comment