Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan sabuwar Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) ta shekarar 2026, a wani mataki da gwamnatin tarayya ta ce zai ƙarfafa tsarin tantance ‘yan ƙasa, inganta tsaro da kuma bunƙasa tattalin arzikin zamani.
An gudanar da bikin sanya hannun a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, tare da halartar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, da Darakta Janar ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote.
Da yake jawabi, Ministan Harkokin Cikin Gida ya ce sabuwar dokar za ta ƙarfafa tsarin tsaro ta hanyar haɗa bayanan hukumomin gwamnati. Ya ce a makon da ya gabata an cafke wasu da ake zargin kwamandojin Boko Haram da ISWAP guda bakwai a Filin Jirgin Sama na Katsina yayin dawowarsu daga aikin Hajji, sakamakon haɗa bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice da kuma tsarin ‘yan sanda na ƙasa da ƙasa.
Tunji-Ojo ya bayyana cewa a baya bayanan gwamnati suna rarrabe, amma yanzu ba za a iya samun fasfo na Najeriya ba sai bayan an tantance bayanan mutum daga NIMC. Ya ce hakan zai ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomi tare da taimakawa wajen yaƙi da satar bayanai, ta’addanci da sauran miyagun laifuka.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yabawa Shugaba Tinubu bisa amincewa da dokar, yana mai cewa za ta taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma ci gaban ƙasa.
A nata ɓangaren, Darakta Janar ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, ta bayyana cewa sabuwar dokar za ta ba Najeriya damar gina ingantaccen tsarin shaidar ɗan ƙasa na zamani, wanda zai sauƙaƙa samar da ayyukan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.