Tinubu ya yabawa Kungiyar ECOWAS bisa jajircewarta wajen karfafa hadin kai da cigaban yankin

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yabawa Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) bisa jajircewarta wajen karfafa hadin kai da cigaban yankin.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jiya talata, yayin bikin kaddamar da wasu muhimman taruka domin bikin cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar ECOWAS, a birnin Accra na kasar Ghana.

A cewar mai taimakawa shugaban kasa musamman kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, Shugaban kasar ya samu wakilcin Bianca Ojukwu, Ministar Harkokin Waje Mai Kula da Jihohi.

Tinubu, wanda shi ne Shugaban Majalisar Shugabannin Kasashen ECOWAS, ya bayyana cewa kungiyar ta ci gaba da bin gwadaben da aka shimfida tun asali, kuma ta zama abin dogaro ga sama da mutane miliyan 400 na yankin.

Ya bukaci kasashen mambobin ECOWAS da su sake duba tsarin kungiyar, ta yadda hada kan al’umma, ba gwamnatoci kawai ba. Ya ce wajibi ne a zuba jari a bangaren ilimi, kirkire-kirkire, da ci gaban fasaha, domin cin gajiyar albarkatun nahiyar Afirka.

A nasa jawabin, tsohon Shugaban Ghana, John Mahama, ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da cewa ‘yan kasa na ji a ransu cewa ECOWAS ba kawai a matsayin wata kungiyar ba ce, amma a matsayin wata kungiya da ke fahimtar burinsu da mafarkinsu.

Comments (0)
Add Comment