Tinubu zai sanya dokar haramta shigo da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin shirya ƙudirin zartarwa a matsayin dokar da za ta hana shigar da duk wasu kayayyaki, ko wata fasaha ko ƙwarewar da ake iya samu a cikin gida.

Takardar wanda ake kira Executive Order a Turance, an umarci ministan shari’a da ya gaggauta shirya ta don gabatar wa shugaban ƙasa ya sanya hannu.

Ministan yaɗa labarai na Najeriya Muhammed Idris ne ya tabbatar da  wannan umarni da shugaba Tinubu zai bayar.

A tattaunawarshi da manema labarai Muhammed Idris ya ce shugaba Bola Tinubu ne ya bada shawarar yin wannan doka a yayin zaman majalisar zartarwa kuma aka amince.

Ya ce an umarci babban lauyan gwamnatin Najeriya Lateef Fagbemi ya shirya wannan doka domin shugaban ya sanya hannu domin ya zama doka.

A ƙarin bayanin da ya yi ministan yaɗa labarai ya ce sabon umarnin na nufin cewa babu dalilin da za a shigo da wani abu Najeriya zarar za a iya samar da shi a ƙasar.

Ya ci gaba da cewa shigo daga kayayyaki cikin Najeriya na haddasa ƴan ƙasar na rasa ayyuka sannan kuma tana rasa kuɗin shiga.

Comments (0)
Add Comment