Shugaban Amurka, Donald Trump, ya caccaki shugaban ɗariƙar Katolika na duniya, Fafaroma Leo, inda ya zarge shi da rauni wajen yaƙi da laifuka da kuma rashin ƙwarewa a harkokin ƙasashen waje.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai, bayan ya wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta, inda ya ce shi ba babban mai goyon bayan Fafaroma ba ne, musamman kan ra’ayoyinsa dangane da rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.
A nasa ɓangaren, Fafaroma Leo ya mayar da martani, inda ya soki kalaman Trump na barazanar rusa al’umma da tarihin Iran, yana mai cewa hakan ba abin amincewa ba ne.
Trump ya ƙara da cewa ba ya jin daɗin yadda Fafaroma ke sukar shugaban Amurka, yana mai cewa da ba shi ne ke jagorantar ƙasar ba, da ba lallai Fafaroma ya kai ga matsayin da yake a yau ba.
A wani saƙo da ya fitar a lokacin hutun Easter, Fafaroma Leo ya buƙaci shugabannin duniya da su kawo ƙarshen tashin hankali, tare da daina danniya da zaluntar al’umma.