Trump Ya Ce Wataƙila da Kansa Zai Halarci Zaman Sanya Hannu Kan Yarjejeniya da Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce akwai yiwuwar ya halarci taron sanya hannu kan yarjejeniya da Iran, wanda aka shirya gudanarwa a ƙasar Switzerland a ranar Juma’a.

A taron manema labarai bayan taron ƙasashen G7 da aka gudanar a Faransa, Trump ya yi watsi da rahotannin wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka da ke cewa Iran za ta samu dala biliyan 300 domin sake gina ƙasar a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

Ya bayyana rahotannin a matsayin “labaran ƙarya”, yana mai cewa, “Ba za mu ba su kuɗi ba. Ba za mu ba su ko sisin kwabo daga cikin waɗannan kuɗaɗen ba.”

A ƙarshen taron manema labaran, an tambayi Trump ko zai ci gaba da zama a Turai domin halartar taron sanya hannu kan yarjejeniyar da Iran. Sai ya amsa da cewa, “Wataƙila.”

Daga nan sai ya yi barkwanci da cewa idan yarjejeniyar ba ta yi nasara ba, zai iya ɗora laifin hakan kan mataimakinsa, J. D. Vance.

Comments (0)
Add Comment