Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya bayar da umarnin sake buɗe sararin samaniyar jiragen kasuwanci na ƙasar Venezuela, abin da ke nuna irin babban ikon da Amurka ke ikirarin yi kan harkokin ƙasar ta Kudancin Amurka.
A yayin wani taron majalissar ministoci da aka gudanar a ranar Alhamis, Trump ya ƙara da cewa ya “sanar” da shugabar riƙon ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez, cewa kamfanonin man fetur na Amurka za su iso nan ba da jimawa ba domin neman damar ayyukan zuba jari a ƙasar.
“Nan ba da jimawa ba ‘yan ƙasar Amurka za su iya zuwa Venezuela, kuma za su kasance cikin tsaro a can. Ƙasar tana ƙarƙashin kulawa mai tsauri,” in ji Trump yayin taron majalissar ministoci a Fadar White House.
Amurka ta yi amfani da barazanar ƙarin hare-haren soji domin tilasta wa gwamnatin Venezuela bin manufofin gwamnatin Trump a muhimman batutuwa, tare da yin watsi da damuwar da ake nunawa kan ikon mallakar ƙasar (sovereignty) na Venezuela.
An rufe sararin samaniyar Venezuela tun kafin Amurka ta kai hari na soji kan ƙasar a ranar 3 ga Janairu, wani farmaki da aka yi wa kallon ya sabawa dokokin ƙasa da ƙasa.
Harin ya kai ga sace tsohon shugaban ƙasar, Nicolas Maduro, da matarsa Cilia Flores, waɗanda daga bisani aka kai su birnin New York domin fuskantar shari’a kan zargin laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
Kamfanin jiragen sama na American Airlines ya sanar da cewa zai dawo da zirga-zirgar jirage zuwa Venezuela bayan Trump ya ce ya umarci Ma’aikatar Sufuri ta Amurka da ta ɗage takunkumin da aka sanya a baya, sai dai hakan na jiran amincewar gwamnatin Trump da kuma tabbacin yanayin tsaro.
Amurka ta dakatar da dukkan jiragen kasuwanci zuwa Venezuela tun a shekarar 2019.