Trump ya sha kaye a Kotun Ƙoli kan dokar zama ɗan Amurka
Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da umarnin shugaban ƙasar, Donald Trump ya aiwatar, wanda ya nemi kawo ƙarshen bai wa jariran da aka haifa a ƙasar izinin zama ‘yan ƙasa kai tsaye.
Alƙalan kotun shida sun amince da hukuncin inda suka tabbatar da cewa haƙƙin zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa yana kunshe cikin kundin tsarin mulkin Amurka, yayin da uku kuma suke da ja.
Donald Trump ya bayyana hukuncin a matsayin “abin takaici” amma ya ce “Majalisar Dokoki za ta iya kafa doka akan hakan.”
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun yi maraba da hukuncin.
A watan Afrilu ne, Mista Trump ya zama shugaban Amurka na farko da ke kan mulki da ya halarci zaman Kotun Ƙoli yayin sauraron shari’ar, duk da cewa ya fice kafin a kammala zaman.