Tsagin Wike Na PDP Zai Gudanar da Babban Taronsa Na Kasa A Ranar Lahad

Babban jam’iyyar hamayyar Najeriya PDP tsagin Nyesom Wike zai gudanar da babban taronsa na ƙasa a ranakun Lahadi da Litinin.

Jam’iyyar PDP – wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida – na ƙoƙarin ɗinke ɓarakarta da ƙwatar mulki a hannun APC mai mulki.

Yuni dai tsagin Kabiru Tanimu Turaki na jam’iyyar ya garzaya kotun Kolin ƙasar da nufin dakatar da hukuncin da ya kwace masa iko da jam’iyyar.

Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ya ziyarci babban filin wasa na ƙasa, inda ake shirye-shiryen gudanar da tarin, ya tabbatar da cewa za a gudanar da taron duk kuwa da ƙoƙarin sansantawa da ɓangarorin biyu ke yi.

Wike ya ce ana sa ran wakilai kusan 2,500 ne za su halarci babban taron, wanda a nan ne za a zaɓi sabbin shugabannin da za su jagorancin jam’iyyar mam da shekara huɗu masu zuwa.

PDP ta faa rikici ne tun gabanin zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa na 2023, lamarin da ya sa wasu ƴaƴan jam’iyyar suka yi fushi.

Haka ma bayan zaɓen jam’iyyar ta rasa mafi yawan gwamnoninta, waɗanda suka koma APC sanadiyyar rikicin jam’iyyar.

Yanzu dai gwamnoni biyu ne kawai suka rage wa jam’iyyar.

Comments (0)
Add Comment