Tsohon Gwamnan Zamfara yana daya daga wayanda suke nuna sha’awar tsayawa takarar Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa

Tohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar, yana daya daga cikin ’yan siyasar da suke nuna sha’awar tsayawa takarar Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa.

Sai dai akwai dimbin kalubale a gabansa da suka hada da rikicin cikin gida da zarge-zargen almundahana da kudin jiharsa.

Daya daga cikin manyan abubuwan da suka cancanci mutum don neman matsayin shugaban jam’iyya ta kasa shi ne gogewa da kwarewa.

Comments (0)
Add Comment