Mun san duk dabarun cin zabe da Shugaba Bola Tinubu ya sani – Babachir Lawal

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa Bola Tinubu da mukarrabansa sun soma nuna damuwa Ya ce suna sane da yadda hadakar ‘yan adawa da tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ke jagoranta ke tsorata APC A cewarsa, akwai ruɗani a cikin fadar shugaban ƙasa saboda irin yadda wannan haɗaka ke ƙara samun karɓuwa a fadin Najeriya.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin kwanciyar hankali sakamakon haɗakar ‘yan adawa.

Haɗakar adawa wacce ta samu jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, na ƙara ƙarfafa gabanin zaɓen 2027.

Babachir Lawal ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ta kebanta da jaridar The Punch, inda ya ce fadar shugaban ƙasa na cikin damuwa sosai da yadda haɗakar ke karɓuwa.

Injiniya Babachir ya kuma kara da cewa Bola Ahmed Tinubu yana iya bakin ƙoƙarinsa domin tarwatsa hadakar ta hanyoyi dabam-dabam.

Comments (0)
Add Comment